Najeriya

Sai nan da wata biyu Buhari zai nada Ministocinsa

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER

Wata majiya da ke kusa da Muhammadu Buhari ta ce shugaban na Najeriya ba zai yi gaggawar nada Ministoci ba har sai ya wanke barnar da gwamnatin da ya gada ta aikata. Jaridun Najeriya sun ruwaito majiyar na cewa sai nan da watanni biyu kafin Buhari ya nada ministocinsa.

Talla

Majiyar tace ko Buhari zai nada ministoci sai zuwa watan Satumba saboda shugaban na kokarin gyara kuran kuran da gwamnatin Goodluck Jonathan ta tafka, domin gina tubalin tafiyar da shugabanci na gari.

Majiyar ta kara da cewa Buhari na nazari akan ma’aikatun da za a rage bisa tsarin gwamnatinsa na rage yawan kashe kudaden gwamnati.

A cewar Majiyar wadanda ke gaggawa a nada Ministoci, ‘Yan siyasa ne da ke neman aikin yi.

Majiyar ta danganta Buhari a matsayin Likita da ke neman magance matsalolin Najeriya.

Wannan dai na zuwa a yayin da Jam’iyyar adawa ta PDP ta ba Buhari wa’adin mako guda ya nada Ministocinsa yayin da shugaban ke cika wata guda da karbar ragamar shugabanci a Najeriya.

A ranar 29 ga watan Yuni ne aka rantsar da Buhari a matsayin Shugaba kasa,yayin da wasu ‘Yan Najeriya suka fara sukar shugaban da rashin sanin makamar aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.