Burundi

Kasashen Afrika za su warware rikicin Burundi

Shugaban Kasar Burundi, Pierre Nkurunziza
Shugaban Kasar Burundi, Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / CARL DE SOUZA

Shuwagabannin kasashen gabashin Afrika zasu sake kaddamar da wani sabon yinkuri a ranar litanin mai zuwa, domin warware rikicin siyasar kasar Burundi.

Talla

Wannan na zuwa ne mako guda da gudanar da zabukan ‘yan majalisun dokoki da na kananan hukumomin Kasar da 'yan adawa suka kauracewa, da kuma kasashen duniya suka yi tir da da shi

Shugabannin kasashen gabashin Afrikar za su gudanar da zaman taronsu ne a ranar litanin domin ganin wata kila su shawo kan shugaban kasar Pierre Nnkrunziza da ya fasa aniyarsa ta neman wa’adi na uku a kan mukamin shugabancin kasar, al’amarin da ya haifar da rikicin siyasar da ya haifar da mutuwar mutane a watanni 2 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.