Faransa-Mali

Sojin Faransa sun kashe wani Kwamandan Al Qaeda a Mali

Dakarun Faransa na musamman da ke kasar Mali sun kashe wani kwamanda na kungiyar al-Qaeda wanda aka saki daga gidan yari a wani musayar fursunoni da aka yi don fansar wani Bafaranshe da ake garkuwa da shi.

Sojin Faransa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali
Sojin Faransa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali .REUTERS/Joe Penney
Talla

Sojan Faransa sun bayyana cewa Ali Ag Wadossene tun lahadi aka kashe shi a garin Kidal da ke arewa maso gabashin Mali, tare da wasu ‘yan ta’adda biyu da ke tare da shi.

Samamen da Dakarun musamman na Faransa suka kaddamar na zuwa ne bayan kazamin hari da kashe sojan kawance na Majalisar Dinkin Duniya su shida, daga kasar Burkina Faso.

Kungiyar Al Qaeda dai ta ce aikinta ne kisan, wanda shi ne mafi muni da aka kai kan Dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali.

Sojan Faransa biyu ne suka rasa rayukansu, a harin Mali da aka kai a ranar lahadi, inda aka jibge sojan Faransa tun shekara ta 2013 domin Korar masu tsananin kishin Islama da suka kwace iko a arewacin kasar.

Shi dai kwamandan al Qaeda da aka kashe na daga cikin wadanda suka rura wutar sace Faransawa biyu a shekara ta 2011

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI