Cote d'Ivoire

An daure dogarin matar Gbagbo

Seka Yapo, dogarin Simone Gbagbo matar tsohun shugaban Cote d'Ivoire
Seka Yapo, dogarin Simone Gbagbo matar tsohun shugaban Cote d'Ivoire AFP / SIA KAMBOU

Wata Kotun soji a kasar Cote d’Ivoire ta yankewa dogarin matar tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari kan laifukan da suka shafi kisa da aka aikata a rikicin da ya faru bayan kammala zaben shugaban kasa a 2010.

Talla

Alkalin Kotun Tahirou Dembele ya ce jami’in Seka Yapo ya aikata laifuka wajen kasha-kashen da aka yi a lokacin, saboda haka ya bada umurnin daure shi a sansanin soji na tsawon shekaru 20.

Dembele ya kuma daure tsohon kwamandan da ke kula sansanin Jami’an tsaro Jean Noel Abehi shekaru 5 a gidan yari saboda tserewa daga wurin aikin sa.

Yanzu haka dai tsohon shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo na fuskantar shari’a a kotun hukunta laifukan yaki a Hague.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.