Mali

'Yan bindiga sun mamaye hotel a Mali tare da kashe mutane

Jami'an Soji a Mali
Jami'an Soji a Mali AFP/PHILIPPE DESMAZES

A kasar Mali mutane hudu sun rasa rayukansu a wani dauki ba dadi da wasu ‘yan bindiga da suka mamaye wani hotel dake tsakiyar kasar tare da yin garkuwa da jama’a. 

Talla

Jami’an sojin biyu sun rasa rayukan nasu ne a fafatawa tsakaninsu da ‘yan bindigan wadanda kuma suka mamaye hotel din mai suna Bybols a sanyin safiyar yau jumma’a, lamarin da jami’an soji harma da mazauna yankin suka bayyana a matasayin yunkurin sace bakin kasashen Turai da suka sauka a hotel din.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar cewa 'yan bindigan na bukatar kama mutane ne domin yin garkuwa dasu kuma rahotanni sun ce Ma'aikatan Majalsar Dinkin Duniya na amfani da wannan hotel din yayin da aka hallaka sojin biyu na dakarun dake aikin tsaro a kewayansa bayaga raunata wadansu uku dabam.

Majiyar ta kara da cewa, an harbe har lahira wani mutum daya yi dammara da bama bamai kana an gana gangar jikin wani mutum farar fata kwance a wajen hotel din.

Har yanzu dai ana ci gaba da fafatawa da 'yan bindigan, inda kuma mazauna yankin suka zauna cikin gidajensu saboda rikicin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI