Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe sojoji 4 a kudancin Najeriya

Matatar mai da tsagerun Niger Delta suka kafa a kudancin Najeriya
Matatar mai da tsagerun Niger Delta suka kafa a kudancin Najeriya AFP
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 1

Hukumomin tsaro a Najeriya sun tabbatar da mutuwar jami’an tsaron kasar akalla 4 sakamakon harin da ake zaton cewa wasu ‘yan fashi akan teku ne suka kai shi barikin soja da ke Nembe a jihar Bayelsa da ke kudancin kasar.

Talla

Shi dai wannan bariki wanda ya kunshi sojoji da ‘yan sanda, babban aikinsa shi ne fada ayyukan fashi akan teku da kuma wadanda ke satar mai.

Wannan ne dai karo na farko da aka kai wa jami’an tsaron irin wannan hari a yankin mai arzikin mai daga lokacin da shugaba Muhammadu Buhari yak arbi ragamar mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.