Za a farfado da masana'antar kera makamai ta Najeriya

Sauti 03:46
Sojojin Najeriya bayan sun kwace sansanin Boko Haram a wani wuri cikin jihar Yobe
Sojojin Najeriya bayan sun kwace sansanin Boko Haram a wani wuri cikin jihar Yobe AFP PHOTO/HO/NIGERIAN ARMY

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin gaggauta farfado da masana'antar kera makamai da ke karkashin ma'aikatar tsaron kasar DICON.Shugaban ya bayyana cewa bai kamata Najeriya ta ci gaba da dogara da kasashen ketare domin sayo makaman da za ta kare kanta ba. Burgediya janar Idirs Bello Dambazau mai ritaya, wani tsohon babban hafsan sojan Najeriya, ya bayyana wa Bashir Ibrahim Idirs muhimmancin farfado da wannan masana'anta ga bangaren tsaron kasar.