Najeriya

Buhari ya nada kwamitin yaki da Rashawa a Najeriya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari statehouse

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada kwamitin bayar da shawara kan yaki da cin hanci da rashawa, don cika alkawarin da ya yi wa al’ummar kasar na dakile matsalar da ke durkusar da ci gaban Najeriya.

Talla

Kwamiti na mutane 7 yana karkashin jagorancin fitaccen lauyan kasar kuma mai rajin kare hakkin Bil Adama, Farfesa Itse Sagay, wanda ake sa ran zai bai wa gwamnati shawara kan hanyoyi da kuma dabarun da za ta yi aiki da su wajen yaki da cin hancin da kuma sauya wasu dokokin da ke yin tarnaki ga yaki da matsalar.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Farfesa Femi Odekunle daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, da Dr Benedicta Daudu da farfesa E. Alemika daga Jami’ar Jos, da Farfesa Sadiq Radda daga Jami’ar Bayero da Hadiza Bala Usman ta kungiyoyin fararen hula, sai kuma Farfesa Bolaji Owasanoye daga Cibiyar horar da ayyukan shari’a.

A wani labari kuma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bukaci bayani kan yadda aka karkatar da Dala biliyan daya da aka ciwo bashi domin gyara hanyar jirgin kasa daga Lagos zuwa Kano.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.