Burundi

Burundi ta la’anci harin da aka kai wa Ma’aikacin RFI

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS

Fadar Shugaban Burundi ta yi allawadai da harin da aka kai wa wani dan jaridan da ke aiki da kamfanin dillancin labarum Faransa na AFP da kuma Radio France International, RFI, wanda jami’an tsaro suka tsare, suka kuma azabtar.

Talla

Esdras Ndikumana, dan kasar Burundi ne mai shekaru 54, yana daukar hotunan wurin da aka bindige wani Janar din sojan kasar ne a birnin Bujumbura ranar 2 ga watan Agusta, jami’an hukumar liken asirin kasar suka kama shi suka yi masa dukan tsiya.

An tsare shi tsawon sa’io 2, lamarin daya sa AFP da RFI suka aike wa hukumomin Burundi da wasikar yin allawadai da lamarin.

Bayan shafe kwanaki 10 da faruwar al’amarin amma sai a jiya alhamis ne mahukuntan Burundi suka yi tsokaci akan abin da ya faru da Dan Jaridar.

A cikin sanarwar da Burundi ta fitar, tace shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya bayar da umurnin a gudanar da bincike domin gano wadanda suka azabtar da Dan Jaridar tare da daukar matakin shari’a akansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.