Guinea Bissau

An bukaci a aiwatar da zanga-zangar tube firaministan Guinea Bissau

Domingos Simões Pereira na Guinea Bissau
Domingos Simões Pereira na Guinea Bissau Liliana Henriques / RFI

Magoya bayan tubabben firaministan kasar Guinea Bissau, sun bukaci a gudanar da zanga-zanga da kuma yajin aikin gama gari, domin tilasta wa shugaban kasar dawo wa da firaministan kasar kan mukaminsa. 

Talla

Magoya bayan Domingos Simoes Pereira wanda aka tube a ranar 12 ga wannan wata, sun ce bai kamata a zura wa shugaban kasar Jose Mario Vaz ido bayan ya tube firaministan saboda dalilai na siyasa ba,

Wannan lamari dai ana ganin cewa zai iya farfado da rikicin siyasa a wannan kasa da ta fi kowace yawan faruwar juye-juyen mulki a Afirka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.