Gabon

Shugaban Gabon ya sadaukar da abinda ya gada ga matasan kasar

Shugaba Ali Bongo na kasar Gabon
Shugaba Ali Bongo na kasar Gabon REUTERS/Luc Gnago

Shugaban kasar Gabon Ali Bango Ondimba, ya ce zai sadaukar da illahirin dukiyar da ya gada daga mahaifinsa tsohon shugaba marigayi Omar Bangon domin tallafa wa matasan kasar ta Gabon.

Talla

Shugaban ya sanar da hakan ne a lokacin da yake jawabi dangane da cikar kasar shekaru 55 da samun ‘yancin-kai a ranar litinin.

Shugaba Bango, ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan da ya samu amincewar matarsa Sylvia Bango da kuma ‘yayansa, inda za’a zuba abinda ya gada daga mahaifinsa a wata gidauniya domin bunkasa ilimin matasan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.