ICC-Kenya

Kotun ICC za ta bayyana matsayinsa akan Kenya

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta Kenyagvt

A yau laraba ne alkalan sashen daukaka kara na kotun hunkunta manyan laifufuka ta duniya ICC da ke birnin Hague, za su bayyana matsayinsu kan rashin samun hadin-kai daga hukumomin kasar Kenya game da zargin da ake yi wa shugaba Uhuru Kenyatta a rikicin zaben kasar da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu daya.

Talla

A watan Disamban bara ne kotun ta duniya ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Uhuru Kenyatta, cewa yana da hannu wajen tayar da rikicin zabe wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu daya da 200 a shekara ta 2007 zuwa 2008.

Sai dai wasu na ganin cewa, rashin samun hadin kai daga hukumomin kasar wajen samun shaidu da za su tabbatar da cewa Kenyatta ya taka rawa a rikicin, shi ne ya sa kotun ta gaggauta yin watsi da tuhumar.

Wasu na ganin cewa kasantuwar Kenyatta shugaban kasa a yanzu kuam kusa a can baya, ya taimaka domin razana wadanda ke son bayar da shaidu a gaban kotu, kuma wannan ne ya sa lokacin da aka fara saurarensa, shaidu suka ki fitowa domin sanar da abin da suka sani dangane da rikicin.

Wani lokaci a can baya dai, daya daga cikin masu binciken wannan batu daga kotun ta duniya, ya ce ofishin mai shigar da kara na gwmanatin Kenya, ya ki karbar wasu daga cikin tambayoyin da masu binciken musababbin faruwar rikicin suka bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.