Najeriya

Najeriya za ta zama ta hudu mafi yawan al'umma a duniya

Rahoton da cibiyar kididdiga game da karuwar jama’a a duniya Population Reference Bureau ta fitar, na nuni da cewa kasashen Afirka ne za su fi samun karuwar jama’a fiye da sauran yankunan duniya.

Karuwar al'umma a duniya.
Karuwar al'umma a duniya. Getty Images/Camille Tokerud
Talla

Kasashen Najeriya, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da kuma Ethiopia su ne za su kasance jagora ta fannin karuwar al’umma kafin shekara ta 2050 idan Allah ya kai mu.

Najeriya a cewar rahoton, za ta ci gaba da ksancewa kasa mafi yawan al’umma a Afirka sannan kuma ta hudu a duniya, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a matsayin ta tara da mutane milyan 190, sai kuma Habasha a matsayin ta goma da mutane milyan 165 kafin shekarar ta 2050.

Rahoton ya kuma ambaci wasu kasashen na Afirka da suka hada da Masar, Tazaniya, Sudan da kuma Uganda, inda adadin al’ummominsu ya ninka har sau biyu, domin kasancewa a cikin kasahe 20 na farko da suka fi yawan jama’a a duniya.

Kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Nijar, za su wayi gari al’ummominsu sun ninka har sau biyu, yayin da rahoton ya jaddada cewa a Nijar ne mace ta fi yawan haihuwa fiye sauran matan duniya, domin mace daya na haihuwar akalla yaro 7 a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI