Najeriya

DSS ta gurfanar da Sambo Dasuki a Kotu

Sambo Dasuki, Tsohon mai ba Shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro a Najeriya
Sambo Dasuki, Tsohon mai ba Shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro a Najeriya REUTERS/Andrew Winning

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta gurfanar da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki a gaban kotu kan tuhumarsa da mallakar makamai ba tare da izini ba.

Talla

Hukumar tace binciken da ta gudanar a gidajen Dasuki guda uku ta gano makamai iri iri wanda haka wani yunkuri ne na zagon-kasa ga tsaron kasa.

Sanarwar hukumar tace bisa ka’idar aiki a karkahsin mulkin demokradiya an gurfanar da shi a gaban kotu don amsa tuhumar da ake ma sa.

A watan Yuli ne jajibirin Sallah, ‘Yan sandan farin kaya suka yi wa Sambo Dasuki dirar mikiya inda suka yi wa gidajensa da ke Abuja da Sokoto bincike kwaf-kwaf.

‘Yan Sandan sun ce sun samu manyan makamai da motoci masu sulke 12 ciki har da na hawa masu tsada wadanda harsashe ba ya iya bulawa guda biyar a samamen da suka kai gidajen Sambo Dasuki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.