Guinea-Bissau

Sojin Kasar Guinea Bissau sun kauracewa siyasa

Dakarun Sojin Guinea Bissau
Dakarun Sojin Guinea Bissau AFP

Dakarun Sojin Kasar Guinea Bissau sun yi alkawarin kauracewa harkar siyasar Kasar kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a yau jumma’a.

Talla

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Kasar, Miguel Trovoada ya shaidawa kwamitin tsaron Majalisar cewa babban hafsan sojin Kasar da wadansu Kwamandoji ne suka tabbatar masa da haka, inda suka ce sun yanke shawarar kauracewa harkar siyasar Kasar baki daya.

Kasar dai ta fuskanci barazanar fadawa cikin rikici bayan shugaba Jose Mario Vaz ya bayyana aniyarsa ta Koran Firaiministansa, sakamakon wasu al-amaura da suka haifar da rashin jituwa da ya hada da sanar da sabon hafsan tsaron Kasar.

A cikin wannan makon ne , Majalisar dokokin kasar ta yi watsi da bukatar Shugaba Jose Mario na neman nada sabon Firaiminista.

Shima dai wakilin Guinea Bissau a Majalisar Dinkin Duniya, Joao Soares Da Gama ya bayyana cewa kawo yanzu Sojojin basu saka baki ba a cece kucen siyasa da ake yi a kasar.

A shekarar 2012, juyin mulkin da Sojin Kasar suka yi ya jefa Guinea Bissau cikin wani hali yayin da ta ke fafutukar farfadowa bayan ta gudanar da zabe a bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.