RFI-Kamaru

RFI na kira ga mahukuntan kasar Kamaru su sako wakilin sashen Hausa

Wakilin sashen Hausa na RFI a Kamaru, Ahmed Abba
Wakilin sashen Hausa na RFI a Kamaru, Ahmed Abba

Hukumar Radio France Internationale ta bukaci hukumomin kasar Kamaru da su bata damar samun bayanai kan wakilin Sashen Hausa, Ahmed Abba da jami’an tsaro suka kama ranar 30 ga watan Yuli na wannan shekarar, a Maroua dake Arewacin kasar.

Talla

Sanarwar da hukumar RFI ta fitar, ta nuna cewar an dauki wakilin daga garin Maroua zuwa Yaounde, don masa tambayoyi dangane da ayyukan kungiyar boko haram a Arewacin Kamaru.

Tuni RFI ta daukar masa lauya Charles Tchoungang, don taimaka masa. Bisa ka’ida a kamaru ‘Yan Sanda ba sa tsare mutum ya wuce kwanaki 28, amma yanzu mun samu bayanin cewar wasu dalilai sun baiwa hukumomi damar tsawaita tsarewar da suke yiwa Ahmed Abba.

Har yanzu Ahmed Abba na tsare ba tare da barin wani yaje inda yake ba, ba kuma tare da barin lauyan sa ya gan shi ba.
RFI ta tsaya kan manufar cewar bashi da laifi, kamar yadda nazarin ayyukan da ya ke yi a shirye shiryen mu suka nuna na rashin nuna san kai.

Saboda haka Radio France Internationale na bukatar sanin halin da wakilin ta ke ciki, da kuma nuna damuwarta akai.

Ganin ya kwashe wata guda a tsare, ya dace Ahmed Abba ya fice daga wannan hali da ya sabawa dokar kasa, dan baiwa lauyan sa damar fahimtar inda aka sa gaba kan lamarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.