Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Burkina Faso-An yi garkuwa da Shugaban Rikon kwarya da Frimiyar kasar

Shugaban Rikon kwarya Burkina Faso Michel Kafando da Kanal Isaac Zida Frimiyar kasar
Shugaban Rikon kwarya Burkina Faso Michel Kafando da Kanal Isaac Zida Frimiyar kasar AFP PHOTO/SIA KAMBOU
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Rahotanni daga Burkina Faso na cewa sojojin da ke gadin fadar shugaban kasar, masu kuma biyaya ga tsohon hambararan shugaban kasar Blaise Compaore sun tsare shugaban rikon kwarya kasar Michel Kafando da firaminista Isaac Zida a fadar shugaban kasar.

Talla

Kakakin Majalisar dokokin kasar Cheriff Sy ya shaidawa kamfanin dilanci labaran Faransa cewa, dakarun da sukayi aiki tare da Blaise Comporea sun kutsa kai cikin Fadar gwamnatin kasar da misalin karfe 2.30 na rana agoggon kasar inda suka yi garkuwa da Kafando da Zida.

Shi ma wakilin Kamfanin dilanci labaran Faransa ya shaida cewa Sojoji sun zagaye fadar gwamnatin kasar.

Wannan al'amari dai tuni ya fara haifar da zanga-zanga tsakanin al’ummar kasar da yanzu haka sojojin ke harba bindiga domin tarwatsa su a birnin kasar na Ouagadougou inda ake garkuwa da Shugaban kasar na rikon kwarya da Frimiyar Kasar.

A watan Oktober shekarar da ta gabata aka hambarar da gwamnatin Blaise Comporea wanda ke gudun hijira a Ivory Coast bayan barkewar rikicin kan zarcewar sa da mulki da ya kwashe shekaru 27 ya na iko.

A halin da ake ciki yanzu dai al’ummar Burkina faso na zaman dar-dar kan rashin sannin makomar wannan al’amari
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.