Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Ana zanga-zanga a Burkina Faso bayan juyin mulki

An yi zanga-zanga a Burkina Faso bayan juyin mulki
An yi zanga-zanga a Burkina Faso bayan juyin mulki AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau | Abdoulkarim Ibrahim
Minti 2

Sojojin da suka kwaci mulki a kasar Burkina Faso, sun kange manyan titunan da ke birnin Ouagadougou fadar gwamnatin kasar, domin hana gudanar da tarzoma kamar dai yadda ‘yan siyasar kasar suka bukaci a yi don nuna adawa da juyin mulkin da sojojin suka yi.

Talla

Tuni dai sojojin suka sanar da rufe iyokokin kasar na sama da kasa, tare da kafa dokar hana fita cikin dare a manyan biranen kasar.

Akalla mutum guda ya mutu, sannan wasu da dama suka jikkata bayan barkewar zanga-zanga a Ouagadougou domin nuna adawa da juyin mulki.

 

Kasashen duniya sun yi tir da kuma allawadai da kwace mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zabe a ranar 11 ga watan gobe.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci Sojojin da suka yi juyin mulki su yi taka-tsantsan

Kungiyar Tarayyar Afirka, da Tarayyar Turai da kuma majalisar dinkin duniya, sun bayyana kwace mulkin a matsayin wanda ya sabawa ka’ida, tare da yin kira ga sojojin da su gaggauta mika mulki ga gwamnatin riko da al’umma ta zaba bayan faduwar gwamnatin Blaise Campoare.

Shugaban Faransa kasar da ta yi wa Burkina Faso mulkin mallaka, Francois Hollande, ya ce kasar ba za ta lamuncewa abin da ke faruwa ba, amma ya ce sojojinsa da ke Burkina Faso ba za su tsoma baki a wannan lamari ba.

A zantawarsa da jaridar Jeune Afrique, janar Gilbert Diendere wanda ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban mulkin soji, ya ce za a saki Michel Kafando shugaban gwamnatin da aka kifar nan ba da jimawa ba, sai dai bai bayyana ko za a saki Firaministan kasar Isaac Zida wanda shi ma ke tsare a hannunsu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.