Isa ga babban shafi
Burkina

MDD ta bukaci Sojin Burkina Faso su saki Shugaban Kasar

Shugaban Kasar Burkina Faso mai rikon kwarya Michel Kafando da Firai Minstansa Kanal Isaac Zida
Shugaban Kasar Burkina Faso mai rikon kwarya Michel Kafando da Firai Minstansa Kanal Isaac Zida AFP/SIA KAMBOU
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Kwamitinn tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi allawadai da yadda Dogarawan shugaban Kasar Burkina faso suka yi garguwa da shugaban Kasar mai rikon kwarya da Firai Ministansa yayin da ya bukaci su gaggauta sakin su.

Talla

A wata sanarwa da mambobin kwamitin 15 suka fitar sun bukaci 'Yan Kasar da su kauce wa tashe tashen hankula yayin da jama’a suka fito kan titunan birnin Ougadougou domin gudanar da zanga zangar adawa da Matakain da Dogarawan suka dauka.

Itama dai kungiyar Tarayyar Afrika AU ta bukaci Dogarawan da su saki shugaban da Firai Ministansa.

A ranar laraba ne Sojojin dake goyon bayan tsohon hambararen shugaban Kasar Blaise Campore suka tsare Michel Kafamdo da Firai Ministansa Kanal Isaac Zida bayan sun kutsa kai a dai dai lokalcin da ake kan gudanar da tarion Majalisar Ministocin Kasar kuma ana kallan al-amarin a matsayin wanda ya yi kama da juyin mulki.

Kawo yanzu dai Sojojin ba su bayyana dalilin daukan matakin ba kuma wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben da zai ba da damar mayar da mulki a hannun farar hula.

A watan Oktoban bara ne wani bore ya yi sanadiyar kifar da gwamantin Blaise Campore bayan ya yi yunkurin yin gyaran fuskka ga kundin tsarin mulkin Kasar da zai bai bashi damar ci gaba da zama kan kujerar shugabancin Kasar da ya shafe tsawon shekaru 27 a kai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.