Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Mutane 100 sun mutu bayan fashewar tankar fetir a Sudan ta kudu

Salva Kiir Shugaban kasar Sudan ta kudu
Salva Kiir Shugaban kasar Sudan ta kudu REUTERS/Goran Tomasevic
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Sama da mutane 100 rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu a Sudan ta Kudu bayan wata tankar mai ta kama da wuta a Juba a yau Alhamis. Rahotanni sun ce kimanin mutane 100 ne kuma ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali wadanda wauta ta kone.

Talla

Wannan al’amari ya auku ne a dai dai lokacin da dururuwan mutane suka yi cikar-kwari domin kwashe man fetur daga cikin motar dakon mai da ta yi hatsari a kan wani yanki da ke yammacin birnin Juba kusa da garin Maridi.

Lamarin da mahukunta yankin da hatsarin ya auku suka ce cunkoson mutane ne ya sa motar ta yi bindiga tare da sanadin hasarar rayuka da kuma jikkata.

Likotoci asibitin garin Maridi da aka kwantar da wadanda hatsarin ya ritsa da su sun ce suna iya kokarinsu domin ceto rayukan wadanda suka kone saboda halin da suke ciki ya tsananta.

Wannan ba shi ba ne karon farko da mutane ke cuncurundo diban man fetir bayan aukuwar hatsarin tankar dakon mai a kasashen afrika, al’amarin da a koda yasuhe ke sanadi rayuka da dama.

Al’amarin kuma na faruwa a yayin da kasar ke cikin yakin basasa tsakanin dakarun gwamnatin Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Reik Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.