Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Sojojin Burkina Faso sun dage dokar hana zirga-zirga

Janar Gilbert Diendéré Shugaban mulkin Soji Burkina Faso
Janar Gilbert Diendéré Shugaban mulkin Soji Burkina Faso AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Bayan share dan karamin lokaci na hana zirga zirga a mayan biranen Burkina faso sojojin da suka kwaci mulki a kasar ,sun sanar da dage dokar ta bace. ‘Yan siyasar kasar na ci gaba da yi kira zuwa kungiyoyin dama fararen fula na tilastawa sojojin janyewa daga madafan ikon kasar.

Talla

Akalla mutum guda ya mutu, sannan wasu da dama suka jikkata bayan barkewar zanga-zanga a Ouagadougou domin nuna adawa da juyin mulki.
Kasashen duniya sun yi tir da kuma allawadai da kwace mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zabe a ranar 11 ga watan gobe.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bukaci Sojojin da suka yi juyin mulki su yi taka-tsantsan
Kungiyar Tarayyar Afirka, da Tarayyar Turai da kuma majalisar dinkin duniya, sun bayyana kwace mulkin a matsayin wanda ya sabawa ka’ida, tare da yin kira ga sojojin da su gaggauta mika mulki ga gwamnatin riko da al’umma ta zaba bayan faduwar gwamnatin Blaise Campoare.

Shugaban Faransa kasar da ta yi wa Burkina Faso mulkin mallaka, Francois Hollande, ya ce kasar ba za ta lamuncewa abin da ke faruwa ba, amma ya ce sojojinsa da ke Burkina Faso ba za su tsoma baki a wannan lamari ba.
A yau ne ake sa ran Shugabanin Kasashen Senegal Macky Sall da Dokta Bony Yayi na Benin za su isa kasar Burkina Faso domin tattaunawa da sojojin .
A zantawarsa da gidan Rediyo Faransa sashen Faransanci, janar Gilbert Diendere wanda ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban mulkin soji, ya ce za a saki Michel Kafando shugaban gwamnatin da aka kifar nan ba da jimawa ba, sai dai bai bayyana ko za a saki Firaministan kasar Isaac Zida wanda shi ma ke tsare a hannunsu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.