Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kira taro kan juyin mulkin Burkina Faso

Janar Gilbert Diendere, Jagoran masu huyin mulkin na Burkina Faso da Shugaba Macky Sall na Senegal kuma shugaban Kungiyar Afrika ta yamma.
Janar Gilbert Diendere, Jagoran masu huyin mulkin na Burkina Faso da Shugaba Macky Sall na Senegal kuma shugaban Kungiyar Afrika ta yamma. AFP PHOTO / AHMED AUOBA
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wani taro na musamman na shugabanin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma kan halin da kae ciki a Burkina Faso.

Talla

Yau ake saran shugabanin zasu tattauna a babban birnin Abuja kan halin da ake ciki da kuma karbar rahotan ziyarar da shugaban kungiyar Macky Sall zai gabatar bayan ya ziyarci kasar.

Sai dai shugaban riko na Burkina Faso Michel Kafando da aka kifar da gwamnatin sa aka kuma tsare shi ya ce bai amince da bukatar da sojojin da suka yi juyin mulkin suka gabatar ba, kuma babu hannun sa a ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.