Isa ga babban shafi
Burkina

Sojojin Burkina Faso sun shiga birnin Ouagadougou

Janar Gilbert Diendere, Jagoran masu huyin mulkin na Burkina Faso.
Janar Gilbert Diendere, Jagoran masu huyin mulkin na Burkina Faso. AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Sojojin Burkina Faso sun kutsa kai birnin Ouagadougou don tattaunawa da masu tsaron fadar shugaban kasar da suka yi juyin mulki game da mayar da shugabancin kasar ga fararen hula.

Talla

Mataimakin shugaban 'Yan Sandan kasar Kanar Serge Alain Ouedrago ya ce daukacin rundunonin sojojin kasar ne suka yiwa babban birnin tsinke a daren jiya, inda suka samu tarba daga fararen hulan dake adawa da juyin mulkin.

Kanar Ouedrago ya ce ana tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkin dan ganin sun ajiye makamansu tare da mika mulki ba tare da zubar da jini ba.

Jakadan Faransa a Ouagadogou Gilles Thibault ya ce yanzu haka shugaban kasar Michel Kafando na Ofishin Jakadancin Faransa bayan an sake shi, yayin da Janar Gilbert Diendere da ya jagoranci juyin mulkin ya nemi gafarar al’ummar kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.