Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Michel Kafando ya fara aiki a wannan laraba

Shugaban rikwon kwaryan Burkina Faso Michel Kafando
Shugaban rikwon kwaryan Burkina Faso Michel Kafando AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
2 Minti

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Burkina Faso Michel Kafando ya ce ya koma kan mulki kasar bayan yunkurin da sojin da ke kula da fadar shugaban kasar suka yi masa.

Talla

Sojojin da suka kwace mulkin  sun Amince da  matakin meka ragamar mulkin bayan share tsawon yinin jiya talata shugabannin kasashen yankin yammacin Afirka na tattaunawa  a birnin Abuja na tarayyar Najeriya, domin samar da mafita dangane da rikicin kasar ta Burkina Faso.

A yanzu dai sojoji karkashin jagorancin Janar Gilbert Diendere, sun amince su koma a cikin barikokinsu bayan da aka ba su tabbacin samun kariya su da iyalansu, yayin da sauran sojojin da ba sa goyon bayan juyin mulki za su fice daga birnin Ouagadougou da akalla tazarar kilomita 50.

A tsakiyar daren jiya ne dai aka gabatar wa Mogho Naba, sarkin kabilar Mossi kuma shugaban majalisar sarakunan kasar da wannan shiri a gaban manema labarai, yayin da janar Diendere ya ce daga wannan laraba Michel Kando shugaban gwamnatin rikon kwaraya da aka kifar zai dawo domin ci gaba da aiki.

Wani lokaci a yau tawagar shugabannin kasashe hudu daga yammacin Afirka za ta isa a birnin Ouagadougou, domin tabbatar da cewa an aiwatar da wannan shiri, kuma majiyoyi sun ce shugaban Senegal Macky Sall, na jamhuriyar Benin Bony Yayi, da shugaban Togo Faure Ngasingbe, sannan da shugaba Mahammadu Buhari na Najeriya ko kuma John Dramani Mahama na Ghana, daya daga cikinsu zai kasance a cikin wannan tagawar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.