Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Burkina Faso ta rusa rundunar sojan tsaron fadar shugaban kasar

Le RSP, corps d'élite de l'armée, était considéré comme la garde prétorienne de l'ancien président Blaise Compaoré. Sa dissolution était réclamée depuis longtemps notamment par la société civile.
Le RSP, corps d'élite de l'armée, était considéré comme la garde prétorienne de l'ancien président Blaise Compaoré. Sa dissolution était réclamée depuis longtemps notamment par la société civile. AFP/SIA KAMBOU

A kasar Burkina Faso an koma wa mulkin rikon kwaryar kasar, kwanaki 5 bayan da shuwagabannin kasashen Afrika suka jagoranci sake mayar da shugaba gwamnatin rikon kwaryar Michel Kafando kan mulki, bayan faruwar juyin mulkin sojan da bai cimma nasara ba, da dogaran tsaron fadar shugaban kasar suka yi a ranar 17 ga watan nan na Satumba da muke ciki.

Talla

A jiya juma’a gwamnatin rikon kwaryar ta gudanar da taron majalisar ministocinta na farko, tun bayan sake darewa kan karagar shugabancin kasar da ta yi.

Matakin farko mai matukar muhimmanci da ta dauka shi ne na rusa rundunar dakarun dake tsaron fadar shugaban kasar dake da alhakin juyin mulkin, rundunar da tun da jimawa kungiyoyin fararen hular kasar suka bukaci rusawa, ganin tsohon shugaban kasar mai gudun hijira Blaise Compaore ne ya kafata.

Tuni dai mai shigar da karar Gwamnatin kasar ta Burkina Faso, ya soma gudanar da binciken gurfanar da duk wanda ke da hannu a yinkurin juyin mulkin na ranar 17 ga watan Satumba shekara ta 2015

Rahotanni daga Wagadugu babban birnin kasar ta Burkina Faso, sun ce kawo yanzu, al’amura na ci gaba da tafiyar hawainiya a kasar, sakamakon yajin aikin gama garin da aka shiga a baya, domin tilasta wa sojojin da suka yi juyin mulkin, maida shi ga hannu wanda suka karba, cewa da Michel Kafando

Kasuwanni da ma’aikatun gwanati na ci gaba da tafiyar da lamurransu a takaitattun lokutta, sakamakon dokar hana fita gida da ke ci gaba da aiki a kasar, duk kuwa da cewar sojojin sun mayar da mulkin a inda suka dauke shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.