Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso sun tsere

An bayyana Sojojin a matsayin masu biyayya ga Blaise Campore, hambararren tsohon shugaban Kasar ta Burkina Faso
An bayyana Sojojin a matsayin masu biyayya ga Blaise Campore, hambararren tsohon shugaban Kasar ta Burkina Faso AFP/SIA KAMBOU

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Burkina Faso sun gudu sun bar barikinsu bayan wani mummunar harin da dakarun dake biyayya ga gwamnatin kasar suka kaddamar dan kwance damararsu.

Talla

Shugaban sojin da ya jagoranci juyin mulkin Janar Gilbert Diendere ya bayyana fargabarsa cewar an jikkata mutane da dama dake zama a barikin ganin irin makaman atilare da dakarun gwamnati suka yi amfani da su kan sojojin nasa.

Su dai Sojojin dake yiwa gwamnati biyayya sun bude wuta ne kan barikin sojin da suka yi juyin mulkin bayan sun ki ajiye makamansu da kuma mika kan su ga jami’an tsaro kamar yadda aka basu umurni.

Janar Pingrenoma Zagre, shugaban rundunar sojin Burkina Faso ya tababtar da kai hare haren da kuma murkushe Sojojin da suka yi juyin mulkin.

Rahotanni sun ce tun ranar juma’a sojojin suka yiwa barikin kawanya, inda aka rufe tashar jiragen saman kasar dake Ouagadogou.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.