Jamhuriyar africa ta tsakiya

ICC ta gargadi mutanen Africa ta tsakiya

Babbar mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Fatou Bensouda.
Babbar mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Fatou Bensouda. AFP

Babbar mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, Fatou Bensouda ta bukaci masu tayar da hankula a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da su daina, inda ta ce za’a hukunta wadanda aka samu da aikata laifukan yaki.

Talla

A cikin wata sanarwa da Ofishinta dake birnin Hague ya fitar, Bensouda ta bukaci kungiyoyin da dai-daikun mutanen dake tayar da kayar baya a kasar da su dakata cikin gaggawa.

Akalla mutane 36 aka kashe a tashin hankalin da ya barke a karshen makon daya gabata bayan hallaka wani Musulmi direban taxi.

Itama dai Shugabar Kasar ta Janhuriyar Afirka ta Tsakiya Catherine Samba Panza ta bukaci al’ummar kasar da su kwantar da hankulansu kuma su koma gidajensu yayin da mutane kimanin dubu 30 suka fice daga babban birnin Bangui sakamakon rikicin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.