Masar

Kotu ta bayar da umarnin sakin 'ya'yan Moubarakh

'Ya'yan Moubarak, Alaa da  Gamal
'Ya'yan Moubarak, Alaa da Gamal REUTERS/Amr Abdallah Dalsh/Files

Wata kotu a kasar Masar yau ta bukaci a sallami ‘ya’yan tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, su biyu da ake tsare dasu saboda zargin cin hanci da rashawa.

Talla

Alkalin kotun ya salami Alaa da Gamal Mubarak saboda kasancewa suna garkame a gidan yari tun shekara ta 2011

Alkalin ya hakikance da cewa zaman da suka yi ya kai adadin zaman da yakamata su yi bisa laifukan da ake zargin su akai

Shekaru uku da suka gabata, bayan kawar da mulkin shugaba Hosni Moubarakh da ya share tsawon shekaru sama da talatin yana mulkin kasar ne aka kama shi tare da ‘ya’yan nasa bisa zargin wawure kuddaden gwamnati da yawan su ya kai dala miliyan 16.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.