GUINEA BISSAU

Sabuwar gwamnati a kasar Guinea Bissau

Shugaban kasar Guinea Bissau Jose Mario Vaz
Shugaban kasar Guinea Bissau Jose Mario Vaz AFP PHOTO / SIA KAMBOU

Hukumomin Kasar Guinea Bissau sun sanar da kafa sabuwar gwamnati bayan kwase watanni biyu ana takun saka a kasar da tayi kaurin suna wajen juyin mulki.Fadar shugaban kasa Jose Mario Vaz ta sanar da cewar sabuwar gwamnatin ta kumshi ministoci 15 da kuma Sakatarori 14, yayin da Firaminista Carlos Correia zai kula da ma’aikatar ma’adinai da kuma na cikin gida.

Talla

Kasar dai na da jam’ar da suka kai miliyan daya da dubu dari shida, kuma Allah ya azirta su da kashew da kifi.
A shekarar 2012, juyin mulkin da Sojin Kasar suka yi ya jefa Guinea Bissau cikin wani hali yayin da ta ke fafutukar farfadowa bayan ta gudanar da zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.