Burkina Faso

An samu hujin alburusai a jikin gawar Sankara

Tsohon Shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara.
Tsohon Shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara. William F. Campbell/Time & Life Pictures/Getty Images

Binciken musabbabin mutuwar tsohon shugaban kasar Burkina Faso, Thomas Sankara da aka kashe a juyin mulkin shekara ta 1987, ya nuna cewa an dirka masa alburusai ne.

Talla

Lauyan iyalan Sankara ne, Ambrose Farama ya sanar da haka a jiya talata, inda ya ce abinda da suka gano dangane da musabbabin mutuwarsa na da tashin hankali, kuma ya ce alburasai sun huhhuda jikin marigayin.

Kusan shekaru talatin kenan da mutuwar Sankara yayinda aka tono gawarsa da na abokansa 12 a watan Mayun da ya gabata a babban birnin Ouagadougou domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsu, inda aka gano ko wanne daga cikin su na da hujin harsashin bindiga a jikinsa, amma na Sankara ya fi yawa, inda ya ke da sama da huji 12 a jikinsa da ya hada da hammatarsa da kirjinsa da kafafunsa.

To sai dai Lauyan ya kara da cewa, iyalan Sankara na dakon sakamakon gwajin gano tsatsaon da mutum ya fito, domin tabbatar da cewa gawarsa ce.

An dai gaggauta binne Saknkara bayan an kashe shi a yujin mulkin da ya bai wa Blaise Campore damar dare wa kan karagar mulki tare da shafe shekaru 27 a kai.

Tuni dai aka yi wa mutane takwas da suka yi yunkurin juyin mulki na baya bayan nan a kasar shari’a dangane da zargin su da hannu a kisan Sankara a wancan lokacin.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.