India

Taron India da kasashen Afirka a birnin New Delhi

Firayiministan India Narendra Modi.
Firayiministan India Narendra Modi. Reuters/Stringer/Files

Kasar India, ta bayyana Afirka a matsayin nahiyar da ke da matukar muhimmancin ta fannin kasuwancin da kuma saka jari a wannan zamani.

Talla

Ministar harkokin wajen kasar Sushma Swaraj wadda ke zantawa da manema labarai a jajibirin babban taro tsakanin shugaban India Narendra Modi da shugabanni Afirka a birnin New Delhi, ta ce Afirka nahiya ce da ke arzikin makamashi da kuma sauran abubuwa na karkashin kasa, wadanda kuma India ke bukata a matsayinta na kasa mai samun habakar tattalin arziki.

Tun a cikin watan disambar shekarar bara ne ya kamata a gudanar da taron amma aka dage shi saboda bullar annobar Ebola a wasu kasashen Afirka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.