Congo

An samu karancin fitowar ma su zabe a Congo

Mutane da dama sun kauracewa zaben raba gardama a Congo Brazzaville
Mutane da dama sun kauracewa zaben raba gardama a Congo Brazzaville AFP PHOTO

Rahotanni daga kasar Congo Brazzaville sun ce masu kada kuri’a da dama ba su fito ba a zaben raba gardamar da aka gudanar a kasar Congo, inda shugaban kasar Dennis Sasso Nguesso ke bukatar sauya kundin tsarin mulkin domin yin wa’adi na uku bayan ya kwashe shekaru 31 a karagar mulki.

Talla

Jam’iyun adawa a kasar sun bukaci magoya bayan su kauracewa zaben kamar yadda Guy Brice Parfait Kolelas ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Sakamakomn kauracewar ya nuna cewar akasarin kuri’un da aka kidaya sun nuna jama’a na goyan bayan sauya kundin.

Shugaba Sassou Nguesso mai shekaru 71 na son ya gyara kundin tsarin mulkin kasar ne domin samun damar tazarce a zaben da da za a gudanar a badi.

A tsarin dokar kasar, an kayyade shekarun dan takarar shugaban kasa zuwa shekaru 70, sannan an kayyade wa’adin shugabanci zuwa biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.