Somalia

Al Shebaab ta kashe Sojin Somalia 30

Somalia na fama da hare haren Mayakan al Shebaab
Somalia na fama da hare haren Mayakan al Shebaab REUTERS/Feisal Omar

Kungiyar Al Shebaab a kasar Somalia ta yi ikrarin hallaka sojojin kasar 30 a wani harin kwantar bauna da ta kai a birnin Mogadishu, kwana guda bayan ta kai wani mummunan hari a wani otel da ke babban birnin kasar.

Talla

Wasu rahotanni na dabam na nuna cewar sojoji 15 suka mutu daga kwantan baunar da mayakan kungiyar suka yi wa dakarun gwamnati.

Amma kakakin kungiyar al Shebaab Abu Musab y ace adadin Sojojin Somalia 30 suka kashetare da kwace manyan motocinsu na yaki sannan suna ci gaba da farautar wadanda suka tsere.

Kasar Somalia na ci gaba da fuskantar tashin hankali duk da kokarin da sojojin Majalisar Dinkin Duniya ke yi na mayar da doka da oda a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI