Saliyo

Saliyo ta rabu da cutar ebola

Cutar ebola ta hallaka mutane da dama a Saliyo da Guinea da Liberia.
Cutar ebola ta hallaka mutane da dama a Saliyo da Guinea da Liberia. REUTERS/Daniel Berehulak/The New York Times/

Ranar Asabar mai zuwa ne ake saran ayyana kasar Saliyo a matsayin wadda ta rabu da cutar ebola bayan an kwashe kwanaki 42 ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba.

Talla

Sai dai har yanzu al’ummar kasar wadda ta rasa mutane sama 4,000 na ci gaba da zaman dar dar ganin yadda cutar ke ci gaba da hallaka mutane a kasar Guinea da ke makwabtaka da ita.

Palo Conteh, shugaban kai dauki kan masu fama da cutar a Saliyo ya ce babu wani biki da za a yi ranar  a Asabar, sai dai kawai farin cikin cewar sun rabu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI