Najeriya

Biafra: 'Yan sanda sun cafke mutane 83

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Solomon Arase
Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Solomon Arase npf.gov

Rundunar ‘Yan sanda a Najeriya tace ta cafke mutane 88 wasu mambobin masu da’awar kasar Biafra a kudancin Najeriya wadanda suka fito wata zanga-zanga domin nuna adawa da kame shugabansu.

Talla

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bayelsa tace tana tsare da maza 78 da mata 5 da aka kame a Yenagoa babban birnin Jihar. Kuma kakakin ‘Yan sandan Jihar yace an cafke su ne saboda suna son tayar husuma da zaune-tsaye a kasa.

Rahotanni daga Bayelsa sun ce ‘yan Biafran sun fito zanga-zanga a wurare hudu inda suka yi arangama da ‘Yan sanda.

Tuni dai rundunar ‘yan Sandan Najeriya ta yi gargadi akan kaucewa gudanar da zanga-zangar bayan masu da’awar Biafra sun shirya gudanar da wata babbar zanga-zanga kan kame shugabansu Nnamdi Kanu da ke yada manufofinsu a gidan Radion da ya bude na musamman kan Biafra.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.