Burundi

Za a fara kwance damar 'yan bindiga a Bujunbura

Pierre Nkurunziza, Pierre Nkurunziza
Pierre Nkurunziza, Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / LANDRY NSHIMIYE

Gwamantin Burundi ta ce daga wannan lahadi jami’an tsaro za su fara aikin kwance damarar ‘yan bindiga a unguwanni na ‘yan adawa da ke birnin Bujunbura.

Talla

A ranar asabar da ta gabata ne wa’adin da aka bai wa masu dauke da makaman ya kawo karshen amma har yanzu ba wanda ya mika nasa makamin.

Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Willy Nyamitwe, ya ce jami’an tsaro za su yi amfani da kwarewarsu domin kwance damarar ‘yan bindigar, yana mai watsi da zargin da wasu ke yi wa gwamnatin kasar na neman haddasa yakin basasa a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI