Senegal

Ana taron zaman lafiya da tsaro a Senegal

An taba gudanar da Taron tsaro a Dakar a 2014 wanda ya hada shugabannin da ke makwabtaka da Senegal
An taba gudanar da Taron tsaro a Dakar a 2014 wanda ya hada shugabannin da ke makwabtaka da Senegal AFP PHOTO / SEYLLOU

An soma taron kasa da kasa kan zaman lafiya da samar da tsaro a Afirka a birnin Dakar na kasar Senegal a yau litinin, a daidai lokacin da kasashe da dama a yankin Sahel ke fama da matsalar tsaro sakamakon ayyukan ta’addanci.

Talla

Taron wanda shi ne irinsa na biyu, zai hada manyan malaman addini da jami’an tsaro da kuma shugabannin al’umma daga sassa daban daban na Afirka.

Kafin buda taron ,jami’an tsaron kasar Senegal sun kai samame a birane da dama da suka hada da Kolda da Rufisque da kuma Khaolack inda suka kama wasu limaman addinin musulunci da dama bisa zargin su da yin alaka da kungiyoyin ta’addanci.

Senegal dai tana makwabtaka da Mali da Mauritania, wadanda ke fama da ayyukan ta’addanci na Alqa’ida da kuma Mujao.

Senegal ta aike da sojoji sama da 500 domin fada da ayyukan ta’addanci a Mali, wannan ya sa ake ganin cewa kasar na cikin hali na barazana daga irin wadannan kungiyoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.