Najeriya

PDP za ta daukaka karar zaben Taraba

Gwamnan Taraba Darius Ishaku na PDP wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben Jihar
Gwamnan Taraba Darius Ishaku na PDP wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben Jihar hausa leadership

Gwamnan Taraba Darius Ishaku ya ce zai daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da kotu ta yanke na soke zabensa a matsayin gwamnan Jihar inda kotun ta bayyana Aisha Alhassan ta APC a matsayin wadda ta lashe zaben.

Talla

A ranar Assabar ne dai kotun sauraren kararrkin zabe a Tabara arewacin Najeriya ta soke zaben gwamnan Jihar Darius Ishaku na Jam’iyyar PDP tare da tabbatar da Hajiya Aisha Jummai Alhassan a matsayin wadda ta lashe zaben na gwamna.

Kotun dai ta soke zaben akan dalilin Jam’iyyar PDP ba ta yi cikakken zaben fitar gwani ba, kafin zaben gwamnan da aka gudanar a watan Afrilu. Amma Gwamnan na Taraba Darius Ishaku yace zai daukaka kara.

Gwamna Darius ne zai ci gaba da jagorantar jihar a matsayin gwamna har sai abinda kotun daukakara ta yanke.

Isa Tafida Mafindi jigo a jam’iyyar ta PDP a can baya a Jihar Taraba yace dalilin da kotu ta yi amfani da na soke zaben Darius a matsayin gwamnan na Taraba shi ne dalilin da ya sa ya fice PDP zuwa APC.

Soken zaben dai ya haifar da barkewar rikici a garin Wukari na Jihar Taraba tsakanin musulmi da kirista inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutane 7, tare da raunata wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.