Chadi

Deby ya kafa dokar ta-baci a yankin tafkin Chadi

Shugaban Chadi Idriss Déby
Shugaban Chadi Idriss Déby AFP PHOTO / MIGUEL MEDINA

Gwamnatin kasar Chadi ta kafa dokar ta-baci a yankunan tafkin Chadi da ya kewaye Najeriya da Nijar da Kamaru kuma ke fama da hare haren ‘yan kungiyar Boko Haram .

Talla

Chadi ta dauki matakin kafa dokar ta-bacin ne bayan wasu mata guda biyu sun kai harin kunar bakin wake a cikin masallaci arewacin Kamaru bayan irinsa da aka kai a Chadi kwanaki biyu da suka gabata.

Ministan sadarwar kasar Hassan Sylla Bakari ya ce dokar za ta bai wa jami’an tsaro Karin karfin gudanar da bincike kan mazauna yankin.

Chadi za ta tsaurara matakan tsaro karkashin dokar inda za a takaita zirga zirgar mutane da ababen hawa tare da gudanar da bincike a gidaje.

Duk da ana samun galaba akan Mayakan Boko Haram da ke da alaka da mayakan IS masu da’awar jihadi a Syria da Iraqi amma sun bullo da salon kai hare haren kunar bakin wake wadanda mata ke kai wa a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.