Bakonmu a Yau

Dr. Yahaya Issoufou kan taron Afrika a Senegal

Sauti 03:33
An taba gudanar da taron tsaro a shekara ta 2014 wanda ya hada da shugabannin da ke makwabtaka da Senegal.
An taba gudanar da taron tsaro a shekara ta 2014 wanda ya hada da shugabannin da ke makwabtaka da Senegal. AFP PHOTO / SEYLLOU

An kawo karshen taro ‘’kan zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka ‘’ wanda ya gudana a birnin Dakar na kasar Senegal inda a tsawon kwanaki biyu masana harkokin tsaro, malaman addinin musulunci da kuma ministoci daga kasashen Afrika da na Turai da dama suka tattauna kan wannan batu.Dr Yahaya Issoufou, masanin ayyukan ta’addanci a jami’ar Yamai, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal yadda yake kallon wannan taro.