Afrika

Wutar lantarki ce za ta bunkasa tattalin arzikin Afrika- shugabanni

Shugabannin Afrika sun ce wutar lantarki ce za ta bunkasa tattalin arzikin nahiyar.
Shugabannin Afrika sun ce wutar lantarki ce za ta bunkasa tattalin arzikin nahiyar. REUTERS/Vasily Fedosenko

Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewar samar da ingantacciyar wutar lantarki ce za ta taimaka wa nahiyar samun ci gaban tattalin arziki da kuma hana mazauna yankin kwarara zuwa Turai don samun rayuwa mai inganci.

Talla

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya bayyana haka yayin ganawa da shugaban kasar Faransa Francois Hollande a birnin Paris kafin taron magance gurbata muhalli da kasar ta Faransa za ta jagoranta a karshen wannan watan.

Mahaman ya ce babban matsalar da ta addabi kasashen Afirka ita ce rashin wutar lantarki, saboda haka abinda suke bukata shi ne hadin kai da kasashen da suka ci gaba.
 

Shugabanin da suka halarci taron sun hada da na kasashen Benin, Guinea, Gabon da Habasha.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI