Masar-Bakin haure

An tsinto Bakin haure ‘yan Afrika 15 a mace a Sinai

Yankin da aka tsinto da Bakin-haure
Yankin da aka tsinto da Bakin-haure REUTERS/Nir Elias

A yau lahadi an gano gawarwaki bakin haure 15 da aka harbe a yankin Sinai na Masar kusa da iyakar Isra’ila kamar yadda jami’an tsaro da kuma jami’an kiwon lafiya a yankin suka tabbatar.

Talla

Tariq Khatir daya daga cikin wakilan ma’aikatan kiwon lafiya da ke arewacin Sinai ya ce gawarwakin bakin 15 da aka harbe ‘yan afrika ne, kuma baya ga su akwai wasu 8 da aka tsinto cikin rauni.

Yankin Sinai da hukumomin masar ke gwabza yaki da mayakan Jihadi, wata hanya ce da bakin haure daga Afrika ke amfani da ita wajen shiga Isra’ila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI