Zimbabwe

Grace Mugabe ba ta da niyyar tsayawa takara

Grace Mugabe,Uwargidan Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Grace Mugabe,Uwargidan Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo

Matar shugaban Zimbabwe Grace Mugabe ta ce ba ta da niyyar tsayawa takarar neman shugabancin kasar domin maye gurbin mai gidanta Robert Mugabe mai shekaru 91 a duniya.

Talla

Grace Mugabe wanda ke gabatar da jawabi a gaban taron mata magoya bayan jam’iyyar Zanu-PF sama da dubu biyar a birnin Harare, ta ce bukatar wannan mukami na shugabancin kasar, ko kuma kokarin tsayawa takara a zabe na shekara ta 2018 a kasar Zimbabwe bai taso ba.
Za ta bayar da goyan baya zuwa mai gidanta Robert Mugabe,wanda ake sa ran gani ya sake tsayawa takara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI