Najeriya

Ba zamu tattauna da ‘Yan Biafra ba- Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari AFP via telegraph

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta zauna kan teburin tattaunawa da wadanda ke fafutukar ballewar wani yanki daga kasar ba. Shugaban ya bayyana haka ne a ta bakin karamin minista a ma’aikatar ilimi na kasar Anthony Onwuka, wanda ya wakilce shi a bikin nada Obi na Onitsha, Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe a matsayin shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Talla

Shugaba Buhari ya ce duk wani batu da ya shafi yunkurin raba Najeriya, abu ne da gwamnatinsa ba za ta taba zaunawa da masu irin wannan ra’ayi domin tattaunawa da su ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka gabatar da Mista Nnmadi Kanu, daya daga cikin jagoran a fafutukar kafa kasar Biafra a gaban kotu, inda ake cajinsa da aikata ayyukan ta’addanci da kuma daukar nauyinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.