Cote d'Ivoire-ICC

Gbagbo yana cikin koshin lafiya- ICC

Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo
Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo AFP PHOTO/ POOL/ MICHAEL KOOREN

Masu gabatar da kara a babbar kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC sun ce tsohon shugaban Cote d’Ivooire Laurent Gbagbo yana cikin koshin lafiyarsa don haka zai gurfana a gaban kotun a ranar 28 ga watan Janairu bayan lauyoyin da ke kare shi sun ce ba shi da lafiya.

Talla

Masanan da suka gudanar da bincike kan lafiyar tsohon shugaban sun ce lafiyarsa lau, babu wata rashin lafiya da ke damun shi, sabanin ikirarin Lauyoyin da ke kare da suka ce yana fama da rashin lafiya mai nasaba da damuwa.

Saboda ikirarin rashin lafiyar Gbagbo ne aka dage sauraren shari’arsa daga 10 ga watan Nuwamba zuwa 28 ga watan Janairu.

Masu gabatar da kara a kotun ta duniya na tuhumar Laurent Gbagbo da aikata laifukan yaki a rikicin Cote d’Ivoire na bayan zaben shugaban kasa da ya ki amincewa ya sauka kan madafan iko a 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.