Zimbabwe

Cutar Sida na Barazana ga rayuwar kanana yara a Zimbabwe

Wani Yaro dake dauke da Cutar Sida
Wani Yaro dake dauke da Cutar Sida © Reuters

Gidauniyar Thomson Reuters ta ce cutar Hiv/Aids Ko Sida har yanzu na daga cikin cututtuka da ke barazana ga rayuwar kanana yara ‘yan kasa da shekaru 5 a Zimbabwe.

Talla

Biciken da hukumar ta aiwatar tsakanin shekarar 1992 zuwa 2012 na cewa duk da kokarin da ake yi da nasara wajen yaki da cutar HIV/AIDS, lamarin a Zimbabwe ya sha ban-ban musamman tsakanin yara.

Akalla kashi 17 cikin 100 na masu shekarun balaga miliyan 1.4 da ke kasar na dauke da cutar HIV da AIDS, kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta rawaito, al’amarin daya sanya kasar da ke kudancin Afrika a cikin mutane 5 mutum 1 na dauke da cutar.

A cewar Shugaban Kungiyar masu dauke da Cutar Sida wato HIV a Zimbabwe Muchanyara Mukamuri, kashi 40 cikin 100 na adadin yara a kasar ke samun rigakafin kariyar cututtuka.

A yanzu dai an kiyasta cewa akalla yara dubu 170 ke dauke da cutar Sida a Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.