Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane sama da 50 cikin kwanaki biyu

Kungiyar Boko Haram ta addabi yankin arewa maso gabashin Najeriya
Kungiyar Boko Haram ta addabi yankin arewa maso gabashin Najeriya REUTERS/Akintunde Akinleye

Sama da mutane 50 suka mutu cikin sa’o’I 48 a hare haren da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa a arewa maso gabashin Najeriya. Wannan kuma na faruwa ne a yayin da wa’adin da gwamnatin kasar ta diba na murkushe mayakan ke kawo karshe.

Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kakkabe Boko Haram a karshen watan Disemba.

Amma cikin kwanaki biyu kafin cikar wa’adin an kai jerin hare haren kunar bakin bakin wake a Jihohin Borno da Adamawa inda mutane da dama suka mutu.

A jiya Litinin ‘Yan mata biyu sun kai hare hare a kasuwar Madagali a Adamawa, kuma kimanin mutane 30 suka mutu.

Kimanin mutane 26 rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwarsu a hare haren da aka kai a Maiduguri a Jihar Borno, 85 kuma suka samu raunuka.

‘Yan Boko Haram kuma sun kai hari a Kauyen Kimba a Borno inda suka kashe mutane 14 tare da kona gidajen mutane a ranar Juma’a.

Akwai wani yunkurin kai hare hare da Sojojin Najeriya suka dakile a Maiduguri a ranar Lahadi.

Kafin cikar wa’adin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace sun samu nasara akan Boko Haram lura da yadda aka tarwatsa kungiyar kuma babu wani gari da ke hannunsu.

Sai dai wasu ‘Yan Najeriya na ganin akwai sauran aiki har yanzu ga gwamnatin Buhari da ta sha alwashin murkushe Boko Haram cikin watanni uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.