Isa ga babban shafi
Najeriya

Cutar Zazzabin Lassa ta barke a Taraba

Bera ke haifar da cutar zazzabin Lassa
Bera ke haifar da cutar zazzabin Lassa wikimedia
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Gwamnatin Jihar Taraba a arewacin Najeriya ta tabbatar da barkewar cutar zazzabin Lassa da ke da nasaba da abincin da Bera ya gurbata da gubar bakin shi.

Talla

Kwamishinan lafiyar Jihar Innocent Vakkai ya tabbatar da mutuwar mutum guda, yayin da aka killace wasu mutane biyu wadanda aka dauki jinin su aka tura Jihar Edo domin gudanar da bincike.

Ana kamuwa da cutar Lassa ne ta hanyar cin abincin da bera ya gurbata ko kuma mu’amala da wadanda ya ke dauke da cutar.

Zazzabin cutar Lassa na yanayi ne da Cutar Ebola mai yin kisa cikin hanzari.

An sanya wa Cutar sunan garin Lassa a cikin Jihar Borno inda aka fara samun bullarta a 1969. Cutar ta bazu a Najeriya zuwa Liberia da Saliyo da Guinea da kuma Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.