Afrika-Asiya

Yammancin Afrika na fuskantar barazanar Cututtuka da Tsun-tsaye ke yadawa

Jerin Tsun-tsaye
Jerin Tsun-tsaye 路透社
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Masana kimiya sunyi gargadi cewa Kasashen Afrika kudu da Sahara da kuma kudu maso gabashin Asiya, su suka fi fuskantar barazanar kamuwa da kwayoyin cututtuka da tsuntsaye irinsu jemage ke yadawa zuwa ga dan adam wanda rigakafinsu ko magani ke da wuyar samuwa.

Talla

Akalla kashi 60 zuwa 75 cikin 100 aka kiyasata cewa na cututtuka da ake fama dasu yanzu na samun asali daga wajen tsuntsaye ko dabobi dawa, musammna Jemage da ake ce na saurin yadda cututtuka daga jikinsa zuwa na dan adam.

Ana dai zargin ire-iren wadannan tsuntsaye da dabobi da yadda cututuuka irinsu Ebola dake saurin kisa, cizon kare da matsalar numfashi da kwayar cutar MERS da ke adaba al ‘umma gabas ta tsakiya da wasu nau’in kuma na cututtuka, da har yanzu ba a ganosu ba.

Masana kimiya a Jami’ar UCL dake London, da kuma masana harkan dabobbi, da Jami’ar Edinburgh na shirin fitar da jerin yankunan dake da hatsari ga bil’adama inda wadanan tsuntsaye sukafi rayuwa.

A cewar Kate Jones na Jami’ar ULC suma al’ummar yankin kudancin Amurka ba a bar su a baya ba domin suna gabar barazanar kawuma da cututtuka da tsuntsaye ke yadawa

A karshe shima Liam Brierley, dalibin a Jami’ar Edinburgh da kuma ke aiki tare da tawagar masu binciken nau’i’ ire-ire cuttuka da tsintsaye ke yadawa ya ce cigaba da samun karuwar cuttuka da tsuntsaye ke yadawa zuwa ga bil adama, ya biyo bayan karuwar adaddin al ‘umma a duniya, dake yadda zango a yankunan da tsuntsaye ko dabobi dawa ke rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.