Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Aubameyang ya lashe kyautar gwarzon Afrika

Pierre Emerick Aubameyang Gwarzon Afrika na kwallon Afrika na shekara ta 2015
Pierre Emerick Aubameyang Gwarzon Afrika na kwallon Afrika na shekara ta 2015 AFP PHOTO/PAUL ELLIS
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Bikin bayar da kyautar gwarzon Afrika ta Ballon d’or da ya gudana a Abuja dake tarrayar Najeriya,Kwarraru dake da nauyin tattance ko zabar dan wasar da ya fi haskawa a duniyar kwallon kafa a Afrika zu zabi Pierre Aubameyang dan kasar Gabon mai shekaru 26.

Talla

Aubameyang na taka leda da kungiyar Dortmund ta kasar Jamus.Aubameyang yayi takara ne da yan wasa da suka hada Yaya Toure dan kasar Cote d’ivoire wanda ya lashe kyautar a shekarar da ta gabata, sai Andre Ayew dan kasar Ghana.
Yaya Toure ya dai lashe wannan kyauta har sau hudu,kamar dan wasan kamaru Samuel Eto wanda ya taba lashe wannan kyauta sau hudu.

Bangaren masu bayar da horo zuwa kungiyoyin wasa,Herve Renard dan kasar Faransa wanda ya taba lashe kopi Afrika da kungiyar Zambia a shekara ta 2012 daga baya ya kuma lashe wannan kopi da kungiyar kasar Cote d’ivoire a shekara ta 2015, shi ya lashe wannan kyauta.
Dan wasa kasar Gabon Pierre Emerik Aubameyang wanda aka fi sani a Jamus da sunan Auba, dan wasan ya dai zura kwallaye 27 a raga a wasani 27 da kungiyar sa ta yi, a dai wajen ana kusan danganta shi da su Christiano Ronaldo dama Messi wajen zura kwallo a raga.

Yaya Toure mai shekaru 32 da haifuwa wanda kuma ke taka leda a Manchester City ya samu kuri’u 136,Andre Ayew dan kasar Ghana mai taka leda a Sweansy City ya tashi da kuri’u 112,gwarzon shekara Pierre Emerick Aubameyang ya tashi da kuri’u143.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.